Hausa
Permanent URI for this collection
Browse
Browsing Hausa by Author "ST Communication"
Now showing 1 - 1 of 1
Results Per Page
Sort Options
Item Masu binciken sun ce ƙwayar cutar ta COVID-19 na iya sauyawa a hankali, ta sa ci gaban rigakafin cikin sauƙi(2023-10-02) ST CommunicationAnnobar cutar COVID-19 tana ci gaba da taɓarɓarewa tun farkonta a ƙarshen watan Nuwamban na shekarar 2019 a birnin Wuhan na ƙasar Sin. Fahimtar da kuma sa-ido a kan yadda ƙwayar halittar ƙwayar cutar take faruwa, yanaye-yanayenta na wuri, da kwanciyar tsayuwarta yana da matuƙar muhimmanci, musamman wajen daƙile yaɗuwar cutar musamman ga samar da allurar rigakafi ta duniya da take rufe dukkan nau’o’in da suke yawo. Daga wannan ra’ayi, mun bincika cikakkun ilahirin ƙwayoyin gadon SARS-CoV-2 guda 30,983 daga ƙasashe 79 da ke cikin nahiyoyi shida kuma muka tattara daga 24 ga watan Disamba 2019, zuwa 13 ga Mayu 2020, bisa ga rumbun bayanan GISAID. Bincikenmu ya nuna kasancewar ɓangarorin rukunoni 3206, tare da rarraba iri ɗaya na sauyi a yankuna daban-daban. Abin sha’awa shi ne, an lura da ƙarancin maimaituwar sauyi; sauyi guda 169 kawai ne (kashi 5.27%) suka sami yaɗuwa fiye da kashi 1% na ilahirin ƙwayoyin gadon. Duk da haka, an gano sauye-sauye goma sha huɗu waɗanda ba a san su ba (> 10%) a wurare daban-daban tare da ilahirin ƙwayoyin gadon ƙwayar cutar; takwas a cikin ORF1ab polyprotein (a cikin nsp2, nsp3, yankin transmembrane, RdRp, helicase, exonuclease, da endoribonuclease), uku a cikin furotin nucleocapsid, kuma ɗaya a cikin kowane sinadaran guda uku: Spike, ORF3a, da kuma ORF8. Haka kuma, an gano sauye guda 36 da ba a san su ba a cikin yankin muhimmin ɓangaren ƙwayar cuta (RBD) na furotin mai kauri tare da ƙarancin yaɗuwa (<1%) a duk nau’o’in ƙwayoyin gadon, waɗanda huɗu ne kawai za su iya haɓaka ɗaurin SARS-CoV- 2 furotin mai kauri ga mai karɓar ACE2 na ɗan’adam. Waɗannan sakamakon tare da bambance-bambancen juyin ƙwayoyin gado na SARS-CoV-2 suna iya nuna cewa ba kamar ƙwayar cutar mura ko ƙwayoyin cutar HIV ba, SARS-CoV-2 yana da ƙarancin sauyi wanda yake ba da yiwuwar haɓaka ingantaccen rigakafin duniya.