UbuntuNet-Connect2024 Registration Now Open: https://ubuntunet.net/uc2024
 

Hausa

Permanent URI for this collection

Browse

Recent Submissions

Now showing 1 - 4 of 4
  • Item
    Matasan Afirka ta Kudu masu HIV da ƙananan CD4 suna da haɗarin kamuwa da cutar daji
    (2023-10-02) ST Communications
    Mun haɗa da daidaikun mutane masu shekaru 15 zuwa 24 daga binciken Match na Cutar Kanjamau na Afirka ta Kudu, babban ƙungiyar da ta samo asali daga alaƙa tsakanin ma'aunin dakin gwaje-gwaje masu alaƙa da HIV daga Sabis na Laboratory Health na Ƙasa da kuma bayanan daga rajistar cutar kansa ta ƙasa. Mun ƙididdige yawan faruwan na mafi yawan nau’ikan cutur daji. Mun kimanta alaqa tsakanin waɗannan cututtukan daji da jinsi, shekaru, shekarar kalanda, da ƙididdigar ƙwayoyin CD4 ta amfani da samfuran Cox da daidaita ma'aunin haɗari (aHR).
  • Item
    Masu binciken sun ce ƙwayar cutar ta COVID-19 na iya sauyawa a hankali, ta sa ci gaban rigakafin cikin sauƙi
    (2023-10-02) ST Communication
    Annobar cutar COVID-19 tana ci gaba da taɓarɓarewa tun farkonta a ƙarshen watan Nuwamban na shekarar 2019 a birnin Wuhan na ƙasar Sin. Fahimtar da kuma sa-ido a kan yadda ƙwayar halittar ƙwayar cutar take faruwa, yanaye-yanayenta na wuri, da kwanciyar tsayuwarta yana da matuƙar muhimmanci, musamman wajen daƙile yaɗuwar cutar musamman ga samar da allurar rigakafi ta duniya da take rufe dukkan nau’o’in da suke yawo. Daga wannan ra’ayi, mun bincika cikakkun ilahirin ƙwayoyin gadon SARS-CoV-2 guda 30,983 daga ƙasashe 79 da ke cikin nahiyoyi shida kuma muka tattara daga 24 ga watan Disamba 2019, zuwa 13 ga Mayu 2020, bisa ga rumbun bayanan GISAID. Bincikenmu ya nuna kasancewar ɓangarorin rukunoni 3206, tare da rarraba iri ɗaya na sauyi a yankuna daban-daban. Abin sha’awa shi ne, an lura da ƙarancin maimaituwar sauyi; sauyi guda 169 kawai ne (kashi 5.27%) suka sami yaɗuwa fiye da kashi 1% na ilahirin ƙwayoyin gadon. Duk da haka, an gano sauye-sauye goma sha huɗu waɗanda ba a san su ba (> 10%) a wurare daban-daban tare da ilahirin ƙwayoyin gadon ƙwayar cutar; takwas a cikin ORF1ab polyprotein (a cikin nsp2, nsp3, yankin transmembrane, RdRp, helicase, exonuclease, da endoribonuclease), uku a cikin furotin nucleocapsid, kuma ɗaya a cikin kowane sinadaran guda uku: Spike, ORF3a, da kuma ORF8. Haka kuma, an gano sauye guda 36 da ba a san su ba a cikin yankin muhimmin ɓangaren ƙwayar cuta (RBD) na furotin mai kauri tare da ƙarancin yaɗuwa (<1%) a duk nau’o’in ƙwayoyin gadon, waɗanda huɗu ne kawai za su iya haɓaka ɗaurin SARS-CoV- 2 furotin mai kauri ga mai karɓar ACE2 na ɗan’adam. Waɗannan sakamakon tare da bambance-bambancen juyin ƙwayoyin gado na SARS-CoV-2 suna iya nuna cewa ba kamar ƙwayar cutar mura ko ƙwayoyin cutar HIV ba, SARS-CoV-2 yana da ƙarancin sauyi wanda yake ba da yiwuwar haɓaka ingantaccen rigakafin duniya.
  • Item
    Yan ƙasar Yuganda masu ɗauke da cutar HIV da hauhawar jini ba sa samun kulawar da suke buƙata
    (2023-10-02) ST Communications
    Mutane Masu Ɗauke da HIV (PLHIV) masu karɓar maganin rigakafi suna ƙara haɗarin kamuwa da cututtukan zuciya (CVD). An bayar da shawar haɗin ayyukan hauhawar jini (HTN), babban haɗarin da ke kawo Cututtukan Zuciya, a cikin asibitocin HIV a ƙasar Yuganda. Ayyukanmu na baya sun nuna giɓi da yawa a cikin aiwatar da haɗin gwiwar kulawar HTN tare da maganin cutar HIV. A cikin wannan binciken, mun nemi yin la’akari da shingaye da masu gudanarwa na haɗa gwajin HTN da magani zuwa asibitocin HIV a Gabashin ƙasar Yuganda.
  • Item
    Za a iya amfani da dabarar X-ray maras gani don taswirar ƙananan gaɓoɓin ƙwari
    (2023-10-07) ST Communications; Philipp, L .; Marion, J.; Du Plessis, A.; Tshibalanganda, M.; Terblanche, J.
    Ƙididdige tsarin numfashi na ƙwari da bambance-bambancensu ya kasance ƙalubale saboda ƙanƙantarsu. A nan muna auna yawan maƙogoron ƙwaro ta amfani da ɗaukar hoton X-ray micro-tomography (µCT) (a haske 15 µm) a kan rayayyun tsutsotsin ƙwaron cerambycid Cacosceles newmannii masu girman jiki mabambanta waɗanda aka yi allurar barci. A cikin wannan takarda mun samar da cikakkun bayanai na bayanan samfur da samfurin 3D don ɗaukar hotuna 12, samar da sabon bayani game da maimaitawa na nazarin hoto da bambance-bambancen halayen maƙogoro da aka samar ta hanyoyi daban-daban na rarraba hoto. Ana bayar da bayanan ƙarar a nan tare da sassan maƙogoro da aka raba a zaman ƙirar 3D.